Hular mutuwa


 A Wani gari anyi Wani yaro,Allah yabawa yaronan wata baiwa🙂‍↕️baiwar kuwa itace,

    Indai mutum yakusa mutuwa to wannan yaron Yana ganewa,shine baiwar da Allah yabashi,

  Ana haka ranar nan sai lbr ya isa zuwa ga sarkin garin nan🫅aka bashi labari akan wannan yaron,sai sarki yace aje azomasa da wannan yaron🧑‍🦱,

     Bayan anzo da wannan yaron sai sarki yace masa ance idan mutum zai mutu kana ganewa? Sai yaro ya gyara zama yace hakane ranka yadade,sai sarki yace Taya kake ganewa?yaro yace ina ganin wata hulane akan mutum,to idan naga hular nan akan mutum to shine zai mutu nan gaba,sai sarki yace yanzu waye zai Kara mutuwa nan kusa? Sai yaron ya ambaci sunan Wani mutum yace shine zai mutu nan kusa, sarki yace shikenan zaka iya tafiya🚶,

     Bayan kwana uku sai wannan bawan Allah ya rasu,hankalin sarki yatashi, Sannan yakara gasgata maganar yaron nan,

      To sai sarki yakira wannan yaron yace masa,yaro idan kaga hular nan akaina kamin magana,yaro yace to ranka ya dade,

   Bayanan an tafi binne gawa a makabarta,ana haka bayan ansa gawa a kabarinta sai kasa ta Dan fallatsi akan sarki, sai yaron nan yace sarki kanka,

   Ai a guje sarki ya Mike yafara zuba gudu😂shi sarki a zatonsa wannan hular aka gani akansa🤣to har yanzu ba'aga sarki ba🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣

Post a Comment

0 Comments